Labarai

Saura kiris mu kawo karshen corona Ganduje

Spread the love

Gwabnan jahar kano Dakta Abdullahi umar Ganduje yayi alfaharin cewa nan ba da jimawa ba za ta kawar da cutar Covid-19 a cikin jihar.

Wannan ikirarin da gwamna Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya yi ya biyo bayan raguwar adadin masu kamuwa da cutar COVID-19 a cikin jihar.

Ganduje ya bayana haka ne a yayin da yakai ziyar duba aikin gyaran Cibiyar killace masu cutar Covid-19 (Yargaya Isolation Center) a ranar Talata, matakan da gwamnati ta dauka ya nuna a fili cewa nan ba da jimawa ba jihar za ta ga bayan cutar.

Ya ce wasu ‘yan shekarun baya da suka gaba ba ta, cibiyar Yargaya ta lalace har wurin ya zama ba’a amfani da shi, Cibiyar anyi amfani da ita Kano, Jigawa da Katsina a lokacin zazzabin Lassa da kuma barkewar cutar Ebola.

Mai ba da gudummawar gyaran Cibiyar a nasa jawabin, Mudasir Idris ya ce ya yanke shawarar aiwatar da aikin ne lokacin da ya ga gwamna Ganduje yana neman taimako a yakar Coronavirus.

Daga Abdulrashid Abdullahi,Kano

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button