Labarai

SERAP Ta Maka Buhari Da Osibanjo A Kotu..

Spread the love

SERAP Ta Kai karar Buhari, NASS; Tana Son Kotu Ta Bayyana Farashin Wutar Lantarki, Karin Farashin Mai Ba bisa Ka’ida ba.

Kungiyar Kare Hakki ta SERAP sun shigar da kara a kan Shugaba Muhammadu Buhari da shugabannin Majalisar Dokoki ta kasa, suna neman kotu ta “bayyana haramtacce, rashin bin tsarin mulki da kuma rashin adalci game da karin kudin wutar lantarki da farashin mai kwanan nan.

Kungiyar ta bayyana cewa manyan jami’an gwamnati ba za su iya ci gaba da karbar albashi da alawus iri daya ba da kashe kudaden jama’a don daukar nauyin rayuwar su ta jin dadi yayin da suke neman talakawan Najeriya da su sadaukar da kai. ”

Wadanda ake kara sun hada da Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, Shugaban Majalisar Dattawa, Dakta Ahmad Lawan, Kakakin Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila, da Hukumar Raya Kudaden, Rabon Kudi da Kasafin Kudi (RMAFC).

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button