
Duk Daliba ko dalibin da ya nemi yayi lalata da malamar sa ko malamin ta to zasuyi Zaman kurkuku na shekara 14.
Babu wasu Dokoki da ASUU ta tanada akan Sexual Harassment.
Majalisar Dattawan Najeriya a karshe ta amince kuma ta samar da doka dangane da malaman dake yiwa daliban su mata barazana ta hanyar neman yin lalata dasu ko kuma su hana masu cin jarabawar su a manyan makarantun gaba da Sakandare.
Idan dai ba’a manta ba wannan dabi’a ta wasu gurbatattun malamai na neman zama ruwan dare wanda ya tilasta dole mahukunta su dauki matakin gaugawa akai.
“Muna so manyan makarantun mu su zama amintaccen wuri ga kowa da kowa” Sen. Ahmad Lawan
Sen. A. Bamidele ya bayyana cewa “kungiyar Malaman Jami’o’i ta kasa ASUU ta yita jaddada mana cewa tana da dokoki masu karfi da suke kula da wannan Sexual Harassment din amma koda muka bincika sai mukaga babu wadannan dokokin”
Saboda haka yanzu shugaban kasa ne kawai muke jira ya sanya ma kunshin dokar hannu daganan shikenan ya zama doka.
Wasu daga cikin abubuwan da kunshin dokar ya kunsa sun hada da:
1-Duk Malami ko Lakcaran da yayi ko ya nemi dalibar sa da lalata ko kuma dalibar da takeso ta shiga makarantar bama ta shiga ba, amma sai ya nemi yayi lalata da ita zai sha dauri na tsawon shekara 14 a gidan Maza, ko kuma daurin da bai yi kasa da shekara 5 ba. Sannan ba tare da biyan tara ba.
2-Duk Malami ko lakcaran da ya umarci ko ya tilasci wani mutum akan ya aikata kowanne irin laifi na sexual harassment, ko aka same shi da hannu a sexual harassment din zai shafe shekara 14 a gidan Maza, ko kuma daurin da bai yi kasa da shekara 5 ba, kuma ba tare da biyan tara ba.
3-Duk Malami ko lakcaran da yayi ma dalibar sa Kiss, ko runguma, ko ya gogi jikin ta, ko ya taba mata Mama, ko ya taba mata gashi, ko leben ta, ko ya taba mata mazaunan ta, ko ya taba mata duk wani wuri mai tada sha’awa a jikin ta, to zai yi zaman gidan kaso har na tsawon shekara 5, amma bazai yi kasa da shekara biyu ba.
4-Duk malami ko Lakcaran da ya baiwa daliba, ko ya nuna mata, ko ya tura mata ta hanyar electronics wasu hotuna ko bidiyo na tsiraici ko wasu abubuwan da suke da alaka da sex to zai iya shafe shekara 5, a gidan Kaso amma daurin bazai gaza shekara 2 ba.
5-Duk wani Malami ko Lakcara ko wani mutumin da yake a wannan cibiyar ilimin sai ya kai report na sexual harassment akan dalibi ko daliba to suma zasu fuskanci hukunci ne daidai da irin wanda aka tanadar wa malaman nasu.
Dan haka aduk lokacin da dalibi ko daliba suka fuskanci Sexual Harassment to suyi gaugawar yin report ga hukumar Makarantar.
Allah ya kyauta, Amin !
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
9th July, 2020.