Al'adu

Sha’awarmu Ga Kudu Maso Gabas Tattalin Arziki Ne Kawai~ Miyetti Allah Ta Fadawa Igbo.

Spread the love

kungiyar Fulani Makiyaya ta Miyetti Allah (MACBAN) ta tabbatar wa ‘yan kabilar Ibo cewa muradin mambobinta ba shi ne kwace musu filaye ko halaka su ba. Ta ce maslaharsu tattalin arziki ne kawai.

Shugaban kungiyar MACBAN a shiyyar, Gidado Siddiki ne ya bayyana hakan a jiya bayan kammala taron hadin gwiwar majalisar zartarwa ta kungiyar a Enugu.

Siddiki ya bayyana cewa bayanin ayyukan makiyayan ya zama dole biyo bayan yawaitar shakku da jita-jita a wasu wuraren.

Ya ce ya zama wajibi a gyara kuskuren tunanin cewa bukatunsu a yankin sun wuce neman tattalin arziki.

Shugaban kungiyar ta MACBAN ya ce, shakkun da ake yi cewa makiyayan suna yin amfani da fadada yankunan Fulani ya rikide zuwa dangantaka mara kyau a sassa da yawa na yankin. Ya ce irin wannan zato ya sa mambobinsu ba su da kwanciyar hankali.

Ya bayyana cewa makiyaya a yankin suna son samun kyakkyawar dangantaka da mutanen yankin.

Kalaman nasa: “Wannan shakkun ya samo asali ne daga jita-jitar da ake yadawa cewa makiyaya suna yin amfani da fadada yankunan Fulani.

”Duk da haka, shugabancin kungiyar ta MACBAN a karkashin kulawa ta a kudu maso gabas ya ci gaba da tattaunawa tare da gwamnatocin jihohin yankin. “Na yi farin ciki cewa tattaunawar ta ba mu fata don kyakkyawar fahimta tsakanin membobinmu da al’ummomin da ke karbar bakuncinsu.” Siddiki ya kuma bayar da tabbacin cewa kungiyar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kai rahoton duk wani mambobinta da aka samu yana da hannu a ayyukan aikata laifi.

Ya yi kira ga gwamnatocin Kudu maso Gabas da su tabbatar da kare mambobinsu da shanunsu, ya kara da cewa za a sa makiyaya a yankin su yi taka-tsantsan yayin gudanar da kasuwancinsu.

Siddiki ya ce, MACBAN ta fahimci cewa kalubalen da makiyaya ke fuskanta ba na yankin ba ne Da yake bayyana mutanen yankin Kudu maso Gabas a matsayin masu kyau, ya yi alkawarin cewa MACBAN ba za ta yi wani abu da zai kawo rikici a shiyyar ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button