Shahararran mai garkuwa da mutane hamisu
Gwamnatin Tarayya ta gurfanar Da Wani kasurgumin Mai garkuwa Da mutane Mai suna Wadume Agaban kotu
Daga Ibrahim Dau Mutuwa Dole
Ajiya Litinin ne Gwamnatin Tarayya ta gurfanar da gogarman masu garkuwa da mutane a jihar Taraba mai suna Hamisu Bala a gaban kotu.
An gurfanar da Hamisu wanda akafi sani da suna Wadume tare da wasu mutane shida, bayan sun shafe watanni goma cur a tsare.
An kama Wadume a Kano, bayan da ya tsere daga hannun ‘yan sanda, lokacin da sojoji suka bude musu wuta a wani gari mai suna Gidan Waya a jihar Taraba, cikin watan Agusta, 2019.
Ajiya Litinin ne bayan Mai gabatar da kara Shuaibu Labaran ya yi wa Mai Shari’a Nyako bayani, ya ce mutanen da ake zargin su 16 ne, amma bakwai kadai suka kama.
Dalilin Haka ne aka rage tuhumar da ake yi musu,daga 16 zuwa 13. Don haka sai ya nemi Mai Shari’a da ya sanya ranar da za a fara sauraren kara ka’in da na’in.
Wadanda aka gabatar din sun hada da Hamisu Bala (Wadume), Aliyu Dadje, Sufeto Umar Bala, Uba Bala, Bashir Waziri, Zubairu Abdullahi da kuma Rayyan Abdul.
Dukkan su bakwai din dai sun shaida wa kotu cewa ba su aikata laifin yin garkuwa, karbar naira milyan 106 kudin fansa, mallakar bindigogi 6 samfurin AK 47 ba tare da lasisin amincewa ba, da sauran su.
Sai dai kuma Sufeton ‘Yan Sanda na Kasa da Ministan Shari’a sun karbi gabatar da Shari’a har an yi masu karin tuhumar su da laifin fashi da kisa.
Kotu ta aza ranar 22 Ga Yuni za a fara sauraren shari’ar gadan-gadan.