Labarai

Shari’ar Vidiyon Dala: Kotu Zata Yanke Hukunci Ranar 22 ga Watan Satumba

Spread the love

A yayin da ake tunanin ganin sunan tsohon gwamnan jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a matsayin minista ko kuma shugaban jam’iyyar APC na ƙasa na wucin gadi, wata sabuwar balahira ta kunno kai.

Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewar wata babbar kotun ɗaukaka ƙara a jihar Kano, ta ayyana ranar 22 ga watan Satumba a matsayin ranar da zata yanke hukunci.

Abisa shari’ar Ganduje wacce take hana hukumar dake kula da hana yiwa tattalin arzikin ƙasa zagon ƙasa da binciken tsohon gwamnan.

Lawyan hukumar da yanzu haka, Femi Falana mai lambar SAN, yayi iƙirarin cewa, kariyar da doka ta bawa Dr. Abdullahi Umar Ganduje ta riga data ƙare tun a 29 ga Mayun data gabata.

Babban lawyan hukumar, ya kuma yi iƙirarin cewa, babu wata kotu a ciki da wajen ƙasar nan da zata iya bawa Ganduje kariya, wanda ya haɗa harda na iyalin sa, ko kuma wani ƙarƙashin gwamnatin sa.

To amma duk da haka, mai lauya mai kare Ganduje ya nace gamida jaddadawa kotu cewar, ba’a bi tsarin doka wajen ba wajen balahirar.

Sannan ya ƙarƙare da cewa, wannan abu da ake yiwa wanda yake karewa, ba komai face keta ƴancin ɗan adam wanda doka da oda ta basa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button