Uncategorized

Shawarar M Inuwa MH…

Salamu alaykum mama Sadiya mai Tallafi ga Shawara….

Daga M Inuwa MH

Amma Wannan Shawara tawa zatayi aikine kadai Idan har da gaske kunaso Sakon naku ya Isa ga Talaka
Game da Nauyin Dake kanki ne na yanzu da Allah ya Dora maki Mama Sadiya mai Tallafi Muna sane da Irin kokarin da kikeyi domin ganin kin gamsar da Al’ummar Nageriya da Tallafin Abinci tare da Kudade wanda Gwamnatin ta Baki Umarnin hakan ta karkashin ma’aikatar da kike Jagoranta, To nidai A Tawa Shawara da tunani Gami da Basirar da Allah ya bani
shine nace wannan Shirin naku me Zai Hana kuyi tsarin anfani bisa ga tura sakonni ta layukan wayar hannu ma’ana dai nasan Zaku iya bibiyar alkaluma tare da Gane talaka Mai Bukatar Taimako ta Hanyar layin Wayar salularsa yawancin Talakawan Nageriya suna da wayar hannu Amma Basu da account Na Banki….

Kowa Yasan talaka bashi iya saka katin waya na yau da Kullum Daya wuce Naira dari 100 Talaka bashi iya kiran waya na yau da Kullum Kuma ya dauki tsayon lokaci Yana wayar wani Talakanma Yana Daukar Wata Guda ba Tare da Ya saka kati a wayarsa ba hakan Zai Tabbatar Maku da cewa wannan Talakane kuma mai Bukatar taimako Zaku iya turama layin talakawan Sakon smg misali kamar haka: Dear Nigerian go to your Poil unit And Collect your N20,000 For COVID-19 donation from….

A Lokacin da Zaku tura wannan Sakon ga talakawan Already Daman Kun Riga Kun Gama tura jami’anku tare da ‘yan sanda Zuwa mazabu Kananan hukumomi tare da Kudaden da Zaku bayarda Tallafin kamar dai yadda ake bayarda katin zabe duk Wanda yazo karbar kudin to lallai yazo da wayarsa Kuma ya nuna Maku Sakon da Gwamnati ta Tura Masa ta Wayarsa kawai Kun gani sai’a bashi kudinsa,
Ni Ina ganin wannan Hanyace Mai Sauki Wacce Mai Bukatar Taimako Zai Iya Samun Taimakonsa Cikin Sauki ba Tare da Wani Ya Cinye Masa kudinsa ba…

Na bayarda wannan shawarane da Zuciya Daya Kuma tsakani da Allah domin tausayina ga Talaka domin Nasan Tsarin da Gwamnati ta Dakko yanzu Ba lallai Sakon ya Kai ga Talaka Mai Bukata taimakon na hakika ba…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button