Labarai

Sheikh Abdujabbar ya Jinjinawa Ganduje Kan saka Ranar mukabalarsa da malaman jihar Kano.

Spread the love

A wani Sakon da Shafin Makarantar Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara Ashabul kahfi warraqeem ya fitar ya nuna jin dadin malamin bisa hukuncin da Gwamnatin Jihar kano ta yanke na zaman mukabalarsu a Ranar 7 ga watan Maris, ga dai Abinda aka rubuta a shafin Makarantar ta malamin cewa… SAKON GODIYA GA GWAMNATIN JIHAR KANO.

Kamar yadda kafar watsa lamarai ta BBC Hausa Suka fitar da rahoto a safiyar nan dangane da ranar da al’umma suke ta jira don tantance gaskiya tsakanin jagoran Mujamma’u Ashabil Kahfi Warraqeem Maulanah Sheikh Dr. Abduljabbar Kabara(H) da Wasu malamai daga mabambantan bangarori da muke dasu a Kano, wadanda suka kai korafi ga gwamnatin Kano gema da tsarin karatunsa, har ma suka datsi wasu sashin karatuttukansa mabambanta suka gabatar a matsayin hujja, wanda hakan yakai ga dakatar da harkokin wannan cibiya tare da rufe masallaci.

Wannan tasa Malam Abduljabbar ya nemi gwamnati ta hadashi zaman Muqabala da wadannan Malamai don tantance gaskiya akan wannan lamari.

Kuma Alhamdulillah ranar Lahadi mai zuwa 7 ga watan Maris, 2021 itace ranar da xa’a gabatar da wannan zama kamar yadda rahotan ya tabbatar.

Muna godiya ga gwamnatin Kano bisa wannan namijin kokari, kuma muna rokon Allah yaci gaba da riko da hannunta wajen tabbatar da adalchi ga kowa.

AKSN
28/2/2021

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button