Uncategorized
Sheikh Abduljabbar ya jinjinawa Ganduje kan hukuncin hadashi Mukabala da malaman jihar kano.
A wata sanarwa da Makarantar Sheikh Abdujabbar Nasiru kabara ta fita yanzu ta nuna jin Dadi game da hukuncin da Gwamnatin Jihar kano ta yanke na hada malaman jihar Kano mukabala da malamin Makarantar ta rubuta ashafin ta na Facebook kamar Haka..
Alhamdulillah, jinjina ga gwamnatin Kano bisa amsa kiran Sheikh Abduljabbar daya dade yanayi na ta hadashi da Malaman da sukai korafi akan tsarin karatunsa su tattauna don tantance ay daga tsakuwa.
Alhamdulillah, wannan babban ci gaba ne, kuma an biyo hanyar adalchi da xata tabbatar da zaman lafiya a wannan jiha tamu dama kasa baki daya.