Labarai

Sheikh Bala Lau ya yabawa Gwamna Uba Sani kan kokarin ‘inganta rayuwar jama’ar jihar Kaduna.

Spread the love

Shugaban kungiyar Jamaatu Izalatil Bida’a wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) na kasa Abdullahi Bala Lau ya yabawa gwamnan jihar Kaduna Uba Sani.

Da yake jawabi a wajen gasar karatun kur’ani da ake gudanarwa kowace shekara a Kinkinau da ke Kaduna, Bala-Lau ya ce Uba Sani ya nuna cewa ya himmatu wajen inganta rayuwar mazauna jihar ta hanyar ayyuka da dama.

Gwamnan Kaduna ya bayar da gudummawar kudi da kyautuka ga wadanda suka yi nasara a fannoni daban-daban a wajen taron.

“Mafi kyawun ‘yan takara guda biyu daga maza da mata za a ba su kujerun Hajji don shiga aikin Hajjin 2024,” in ji gwamnan.

Sani ya bukaci mahalarta gasar da su sanya koyarwar kur’ani a cikin harkokinsu na yau da kullum.

Ya kuma bukaci musulmai da su rungumi hikima da shiriyar Al-Qur’ani, saboda karfin kawo sauyi da yake da shi a kowane bangare na rayuwa.

Gwamnan Kaduna ya sanar da cewa an kafa kwamitin da zai magance matsalolin da aka fuskanta yayin aikin Hajjin da ya gabata.

Ya nuna rashin jin dadinsa da “yanayin rashin sa’a” da aka rubuta a lokacin aikin Hajjin da ya gabata.

Sani ya kuma ce ya yi gargadi ga mutanen da suka je masa Neman kwangilar ciyar da alhazai, inda ya ce duk wanda ya damfari alhazai zai gamu da fushin Allah domin ana amsa addu’ar wadanda aka zalunta ba tare da shamaki ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button