Sheikh Gumi ya nemi Gwamnati da ta yiwa ‘Yan Bindiga gafara.
Shahararren malamin addinin Islama, Sheikh Gumi, ya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta bada dama ga ‘yan fashi da ke son yin sulhu idan har za a magance matsalar tsaro a yanzu.
Malamin addinin Islama ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin da yake zantawa da manema labarai a Minna, babban birnin jihar Neja.
Wannan ya faru ne bayan malamin ya ziyarci sansanin wasu ‘yan fashi da ke aiki a jihar Neja.
Ya bayyana cewa wasu korafe-korafen ‘yan fashin shine ana kashe su tare da nakasa su ba da hakki ba.
Da yake magana game da tattaunawar da ya yi yayin ziyarar sirri da ya yi da ‘yan ta’addan, Sheik Gumi ya ce akwai kyakkyawan martani daga ‘yan bindigar da ke garkame da daliban makarantar Kagara da ma’aikatansu.
Amma bai bayyana ko an saki daliban ba.
Kalaman na Gumi na zuwa ne ‘yan kwanaki bayan da‘ yan bindiga suka samu damar shiga Kwalejin Kimiyya ta Gwamnati, Kagara, karamar hukumar Rafi ta jihar Neja da misalin karfe 2:00 suka yi awon gaba da dimbin dalibai, malamai da wasu da dama.
Shugaban makarantar da ya tsere daga harin ya tabbatarwa da gidan Talabijin na Channels cewa aikin ya fara ne daga gidajen ma’aikata inda suka sace wasu ma’aikatan ciki har da wasu ma’aurata kafin su samu damar shiga gidajen kwanan daliban.