Sheikh gumi yana sulhu da ‘yan ta’adda ne domin Buhari da Gwamnatin sa zun Gaza ~Inji Shehu Sani.
Tsohon dan majalisar dokokin Najeriya, Shehu Sani, ya ce, mashahurin a Nazarin Addinin Musulunci, Sheikh Gumi yana ganawa da ‘yan fashi ne a duk fadin jihohin saboda gwamnatin Shugaba Buhari ta kasa kare‘ yan kasarta daga harin ‘yan fashi.
Sanata Shehu sani a cikin wani sako a shafinsa na Twitter a ranar Asabar, 20 ga watan Fabrairu ya ce Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya da gwamnatinsa sun gaza matuka kuma hakan ne ya bawa Gumi damar Shiga sulhu da ‘yan ta’adda Inji Shehu Sani
Sakon na Twitter din nasa yana Cewa “Idan da Gwamnati ba ta yi kasa a gwiwa ba wajen tsare rayukan mutane, da ba a sami sa hannun Sheikh Gumi ba. Kawai sai ya shiga wani hali. ”
Bayanin na Shehu Sani ya biyo bayan cece-kuce ne game da ziyarar Gumi zuwa sansanonin ‘yan fashi a Zamfara da Jihar Neja kwanan nan.
Shehin malamin ya sanya kanun labarai a kan kiransa na yin afuwa da tattaunawa da ‘yan fashi.