Labarai

Sheikh Idris ya yi wa su Sheikh Bala Lau Allah ya Isa kan Zuwa wajen kauran bauchi domin bayarda hakuri.

Spread the love

Sheikh Idris dutsen tanshi ya bayyana hakan ne a wani zaman Majalisinsa Jim kadan bayan ya fito daga gidan kurkuku Yana Mai cewa labari ya isheni cewa wata kunguya Shugabannin ta za su taso zu zo bauchi a kan wai ayi maganar a sake ni da naji haka sai nace a Fadawa wakilina tunda ni ba’a waje nake ba cewa a fada masu bana bukatar su sa Baki a case Dina Kuma idan suka sa Baki Allah ya Isa.

Alhamdulillah na sanar da Ibrahim disina na Kuma sanar da Datti Assalify naji ance yayi rubutu cewa bana son Wani Dan Kungiya ko Malamin Kungiya ya sa Baki meyasa bana so? Malamin yace idan Baku manta maganar Pantami ba lokacin da aka kaini DSS  yazo yace zaiyi belina nace indai belinka ne na mutu a hannun DSS sai yace a a bashi ne yazo belina ba Shima Dan aika ne ga wanda ya sakashi.

Amma dukda haka da wata matsala ta faru na Dan zungure shi sai almajiransa suka ce mutumin Daya fito dakai? Yanzu bana son a maimaita irin wannan kar bayan Allah yayi ikonsa na fito wata Kungiya tazo tayi Alfahari, tace ai Ina sukan Kungiya Amma da aka kamani ai sai Kungiya ta Saka Baki na fito.

Sheikh Idris dutsen tanshi na fuskantar Tuhume Tuhume daga hukommi da dama a jihar Bauchi duk a kan batun Kalamai da zargin tayar da tarzoma tsakanin Al’umma.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button