Sheikh Pantami Yana Girman kai…
Marubucin Shine Dr Sharif Almuhajir yana cewa
Shawara Ga Dr Pantami
Na gane cewa gaskiyar magana akwai bukatar wasu daga cikin dattawan Arewa ko shugabannin addini, ko na sarauta ko na siyasa su zauna da Dr Isa Ali Pantami domin su ja hankalin shi.
Na fahimci yawancin manyan y’an siyasa suna zargin shi da girman kai da rashin tawali’u da bubbudawa a gaban wadanda suka haife shi a shekare, suka riga shi shiga siyasa, Kuma suka fi shi bada gudunmawa a zuwan gomnati.
Sannan wasu cikin ma’aikatan shi suna zargin shi da wulakanci da karancin hakuri, wasu cikin abokan shi na karatu da aiki suna zargin shi da ko-in-kula da kusancin su wajen rashin zumumci, daliban shi na Bauchi kam tuni yayi ba kwana da su.
Babu shakka ba dukkan korafi ne ke zama daidai ba, amma ina gani ba zai zama matsala ba idan aka samu wadanda za su nusantar da shi saboda ya gyara muamalar shi da mutanen da ke kusa-kusa da shi.