Tsaro

Shekau Yana Cikin Sansanin Sojoji Sheikh Zakzaky

Spread the love

Yau Shekaru Shida Kenan da Malam Zakzaky yayi Wannan Hasashe Inda Yake Cewa Shekau Yana Boye Cikin Sansanin Sojoji, Cewar Sheik Zakzaky.

Sanannen malamin addinin nan da ke garin Zaria a jihar Kaduna, Sheik Ibrahim El-Zakzaky ya bayyana a ranar Asabar da ta gabata cewa rundunar sojojin Nijeriya sun fi kowa sanin inda shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau yake. Inda Shehin malamin ya kara da cewa Shekau yana boye ne a sansanin sojojin kasar nan, ba wai a kasar waje ba.

Ya kuma yi kira ga rundunar sojojin da su daina yawo da hankalin al’ummar Nijeriya, domin babu wani abu makamancin Boko Haram, kawai ana so a yi amfani da wannan ta’addancin ne a tarwatsa Nijeriya.

Ya kara da cewa bayan kudurin da ake da shi na tarwatsa kasar, Boko Haram wani makami ne ga kasashen Turawa don su shigo Nijeriya kamar yadda suka yi a sauran wasu kasashe don samu su mamaye arzikin kasar.

A Lokacin Da Yayi wannan batu Yan shi’a mabiyansa dama wasu sun gaskatashi sosai to amma sai dai haryanzu batun nasa be tabbata ba…

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button