Shi ne mutumin da ya yi silar samuwar Jirgin Sama a Duniya ‘Abu Al’qasim Abbas Ibn Firnas Wirdas Al’takurini.
Abbas bin Firnas shi ne Ɗan’adam na farko a duniya da ya fara gwada tashi sama ta hanyar haɗa wani ƙ’aramin Firem na Inji, a yau shekara sama da dubu ɗaya da ɗari ɗaya 1100 kenan.
Da farko dai wani mutumin ƙasar China ne ya fara tunanin fara yunƙurin ƙera Inji da zai tashi sama da Ɗan’adam a wajejen ƙarni na biyar, amma hakan bai samu ba, har sai bayan shekaru dari uku 300 da wancan yunƙuri da mutumin ƙasar China yayi sai aka sami mutumin ƙasar Cordova Abbas bin Firnas ya cimma wannan Yinkuri.
Abbas bin Firnas an haife shi ne a ƙauyen Izn-Randa Onda na garin Qutuba Al’andalus Cordova wanda yanzu haka ita ce ƙasar Spain, kuma ya yi rayuwarsa ne cikin daular Cordova wanda ɗaya ce cikin daular Musulunci a Duniya, Amma Abbas asalin iyayensa ƴan ƙabilar ‘Berber’ ne da suka fito daga arewacin Afirka inda ƙashashen Morocco da Algeria su ke.
Masana Ilimin Kimiyyar ƙere-ƙere sun rubuta cewar Abbas bin Firnas shi ne Mutum na farko da ya fara Silar ƙera jirgin sama ya tashi sama (Aeronautics), Kuma mutum ne mai ilimin harhaɗa Maganunuwa (Medicine) gashi kuma Injiniya ne, domin a wancan lokacin Cordova da garin Bagdad Manyan cubiyoyin koyon aikin Injiniya, da tsara gine- gine (Architects) da ilimin fasaha, kuma tun yana ƙarami Abbas bin Firnas ya karanci fannonin ilimin na fasaha, Amma kuma ya fi sha’awar Fannin Injiniya da yake ƙirkire-ƙirkire da kansa, yana kuma ƙaunar Kiɗe -kiɗe da kuma wakokin baƙa na Larabci.
Tun a shekara ta 852 Abbas ya fara gwada tashi sama ta hanyar tsalle a Hasumiyyar Masallacin Qurtuba na yankin Cordova, inda ya tashi sama kamar tsuntsu kuma Mintuna 10 da tashin sa sai ya faɗo ƙasa ya samu rauni a bayansa, daga baya Abbas ya fahimci kura-kuren da ya samu a tashinsa na farko, daga nan kuma sai ya ɓullo da sabbin hanyoyin Irin su amfani da Jelar jirgi da gilashin fuska da Inji da ke auna zafin ruwa (water clock) da dai sauransu.
Tun daga wancan lokacin ne Abbas bin firnas ya cigaba da ɓullo da fasahar ƙere-ƙere ta hanyoyi daban-daban.
Yanzu haka dai akwai wurare da dama da aka sanya sunan Abbas bin Firrnas, kuma daga cikinsu akwai filin jirgin sama na Birnin Bagdad na Kasar Iraq.
Daga Mutawakkil Gambo Doko.