Rahotanni

Shikenan Ma: Gwamna El-Rufa’i Ya Kawo Hanyar Da Za A Bi A Magance Fyade.

Spread the love

Daga:- Aliyu Adamu Tsiga

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasir el-Rufa’i ya ce babbar hanyar magance matsalar fyade ita ce yiwa masu aikata laifin dandaqa.

Malam Nasir ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar ta bidiyo ta manhajar Zoom ranar Asabar.

An yi taron ne da nufin lalubo hanyoyin magance matsalar fyade da ta ki ci ta ki cinyewa a kasarnan.

Gwamnan ya ce cikin harshen Turanci wanda da shi aka gudanar da taron “Remove the tools”, wato a cire kayan aikin.

Sannan gwamnan ya ce a jiharsa ta Kaduna an samu karuwar fyade inda aka yi wa mutum 485 cikin kankanin lokaci a baya-bayan nan, kamar yadda alkaluma suka nuna.

Baya ga gwamnan jihar Kaduna, akwai ministar harkokin mata da shugabar hukumar NAPTIP da matan gwamnonin jihohin Niger da Kaduna da Kebbi.

Sauran mahalartan sun hada da ‘yan jarida da masu fafutuka da wakilan kungiyoyin Kare hakkin bil’adama da kuma lauyoyi.
Me sauran masu ruwa da tsaki suka ce?

Malam Nasiru ya ce a cire kayan aiki a kuma dinga yanke hukuncin daurin rai da rai kan masu aikata fyade.

Ya kara da cewa akwai bukatar iyaye mata su dinga tarbiyyantar da ‘ya’yansu maza wajen ganin girman mutuncin mace da gudun keta haddinta.

Ita kuwa ministar mata Pauline Tallen ta fadi abubuwan da gwamnati ke yi na kokarin hada karfi a ciki da wajen kasa don yakar fyade.

Matar gwamnan jihar Niger Mrs Lolo kuwa bayani ta yi a likitance kan yadda macen da aka yi wa fyade ke shiga uku ko da bayan ta girma ta yi aure.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button