Labarai

Shin da gaske ne kasar Amurka na neman Atiku ruwa a jallo?

Spread the love

Daya ke Magana ta Bakin Mai taimaka masa a harkokin Sadarwa Tsohon mataimakin Shugaban Kasa Alh Atiku Abubakar Yace bashi Acikin jerin wa’yanda kasar Amurka ke bibiya tana sa musu mataimakin nasa Yace kasar Amurka Bata tuhumar
ATIKU da komai Haka zalika kuma ma’aikatar shari’ar Amurka Zuwa wasu kasashen Babu masu tuhumar sa da Laifin komai Idan za a iya tunawa, an taba ire iren wadannan karairayin a gabanin zaben shugaban kasa na ranar 23 ga Fabrairu, 2019, Kan cewa ATIKU bashi da damar da zai iya Zuwa Amurka.


ATIKU Abubakar ya nemi bizar Amurka Kuma Amurka ta bashi inda ya fara ziyarar Amurka a watan Janairu 17, 2019. Ya sauka a wani otal mai nisan mil kaɗan zuwa Sashin Shari’a na Amurka. Abubakar a yayin wannan tafiyar ya samu karbuwa daga jami’an Gwamnatin Amurka .

Ana so a karkata Hankalin Yan Najeriya ne daga maganar da Sakataren Gwamnatin Amurka, Mista Mike Pompeo ya yi a kwanan nan, na haramta biza da saka takunkumi ga wasu mutane da sanannu na Jam’iyar APC ga Kuma yadda suka Sha kunya a zaben gwamnan jihar Edo,
Lallai ya kamata mutane suyi tunani Kan ire iren Bata gari masu son Bata sunan atiku Abubakar Inji Paul Ibe, Mai taimaka wa Atiku Abubakar ta fuskar yada labarai.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button