Rahotanni

Shin Dagaske Ne Baturiyar Nan ‘Yar Kasar Amurka Wadda Tazo Wajen Saurayinta Dan Jihar Kano Ta Rasu?

Spread the love

Daga Sabiu Danmudi Alkanawi

A safiyar yau ne daya daga cikin Editocin Jaridar Mikiya Sabiu Danmudi Alkanawi yaci karo da wani labari da yake yawo a shafin Facebook wanda yake shelanta rasuwar Baturiyar nan Jeanine Sunchez wadda ta taso takanas tun daga Kasar Amurka zuwa jihar Kanon Najeriya domin ganawa da masoyinta kuma rabin ranta wato Sulaiman Isah Panshekara.

Masu shelanta rasuwar Jeanine Sunchez sunce ta rasu ne sakamakon zazzabi mai zafi da tayi fama dashi.

Da ganin wannan labari nan da nan Alkanawi yabazama wajen neman Sulaiman Isah Panshekara domin yaji gaskiyar labari, Alkanawi ya yi nasarar samun Sulaiman Isah Panshekara a waya, inda ya shaida masa halin da ake ciki.

Sulaiman Isah Panshekara ya nuna rashin jin dadinshi game da yadda Mutane kirkirar labarin karya akan masoyiyarsa abar kaunarsa, ya kara da cewa wannan labarin bashi da tushe balle makama, domin kuwa masoyiyarsa Jeanine Sunchez tana nan cikin koshin Lafiya….

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button