Shin Dan Sanda Yana Da Hurumin Da Zai Tsareka A Hanya Ya Cajeka?
Shin Police yana da Hurumin da zai amshe Wayar ka Ko Laptop dinka yayi Searching din su ?
-Shin Police yana da Hurumin da zai shiga gidan ka yayi bincike?
Police ko kuma dan Sanda, wani jami’in tsaron gwamnati ne da aka samar domin ya kiyaye rayuka da dukiyoyin al’umma. Sannan suna da dokoki da suke gudanar da ayyukan su akai. (Police Force, Act)
Saidai a wasu lokutan akan samu matsala tsakanin Jama’ar gari da su jami’an yan sanda ta bangaren bincike, inda Jami’an ‘yan sandan suke ganin cewa su aikin su suke yi, a dayan bangare kuma mutanen gari suna ganin wannan cin zarafi ne, ba aiki ba.
To saidai akwai tanadin da dokar yan sanda ta kasa tayi akan binciken mutum (wato searching/stop and search).
Sashi na 29 na dokar ‘yan sanda ya basu damar su tsare mutum suyi searching din sa idan har suna zargin sa da wani abu na laifi
To saidai wannan ba shine zai basu damar suci zarafin ka ba, a ka’ida zasu fara yimaka tambayoyi ne akan abunda suke zargin ka dashi, idan ka amsa masu duka tambayoyin yadda ya kamata to anan ba suda hurumin da zasu yi Searching din ka, idan ma za suyi searching din naka to dole sai sun fada maka abunda suke zargin ka dashi.
(Akwai wani malami a kasar nan da suka tsare shi akan hanyar sa ta zuwa Abuja sukace zasuyi searching shikuma yace to su fada masa abunda suke zargin sa dashi sannan ya basu damar yin searching din motocin nasa, to akarshe dai haka sukayita rigima)
To idan kuma sukayi searching din naka a haka bayan ka amsa tambayoyin su, kokuma basu sanar maka abunda suke zargin ka dashi ba, to wannan shi ake kira illegal search (haramtaccen bincike).
Dangane da Police ya tsare ka ya amshe wayar ka ko Laptop ko Email Address ko Messages ko hotunan wayar ka yayi searching akai, ehh yana da hurumin yin hakan amma dole sai ya nuna maka takardar izinin kotu akan yayi wannan binciken. Wannan takardar ita ake kira (Search Warrant) idan har yayi seaeching din bayan bai nuna maka Search Warrant din ba wannan shima haramtaccen bincike ne (Illegal Search).
A bangaren kuma dan sanda ko wani jami’in tsaro ya shiga gidan ka yayi bincike to shima doka ta basu dama, amma dole sai sun nuna maka takardar izinin yin hakan daga kotu, idan ba haka ba to shima wannan illegal Search ne.
ME YA KAMATA KAYI A DUK LOKACIN DA AKA YIMAKA ILLEGAL SEARCH ?
To, na farko dai illegal Search ya saba da sashi na 29 na dokar ‘yan sanda ta kasa (Police Force, Act) haka kuma ya saba da Sashi na 34 (1) (a), da kuma Sashi na 35 (1) da kuma Sashi na 37 da Sashi na 42 (1) duka na dokar kasa (Nigerian Constitution 1999 as amended)
Ga matakai 10 da ya kamata kabi aduk lokacin da hakan ta faru
1-Ka tambayeshi dalilin yin Searching dinka/ gidan ka/wayar ka/ko laptop din ka.
2-Ya nuna maka takardar izinin kotu akan binciken gidan naka/wayar ka/laptop dinka. (Amma idan kaine karan kanka ba sai ya nuna maka Search Warrant din ba)
3-Kar kayi jayayya ko rigima dashi
4-Kayi Kokarin gane suna da lambar dan sandan da ya bincike ka din
5-Ka rike lambar motar da suke Patrol din da ita
6-Ka tambayeshi ya fada maka ko shi wanene, idan ya saka kayan gida ne
7-Idan sun jimaka rauni kayi kokari ka dauki hotunan wurin
8-Kayi kokarin samun shaidu
9-Ka amsa masu duka tambayoyin su gwargwadon sanin ka
10-Idan suka ce su Searching dinka zasuyi ka fada masu ba suda wannan hurumin tunda ka amsa masu tambayoyin su yadda ya kamata
11-Idan suka dage sai sunyi searching din naka to ka barsu suyi amma ka fada masu zaka tafi kotu don abi maka hakkin ka.
12-Akarshe idan sun sake ka sai kaje ka samu Lawyer kayi masa bayanin yadda abun ya faru (akwai Legal aid Council) wadanda ba sai ka biyasu ba su zasu tsaya maka kyauta dan ganin sun kwato maka hakkin ka.
Bissalam
Shehu Rahinat Na’Allah
10th August, 2020