Rahotanni

Shin Kuɗi Yafi Maka Ran Ɗan uwanka?

Spread the love

Hakika Kuɗi wasu Takardu ne Masu Daraja dake zama shaida, Yayin Musayar Albarkatun da Allah Ya Azurtamu dasu.

Saidai Ya kamata Mugane cewa Darajar tasu, Bata kai Albarkatun namu ba, saboda Dan Adam ne ya Ƙirƙire su, sannan kuma Ba’a sakawa A Baki Aci amatsayin Abinci, kokuma suyi aiki da kansu.

Hakan Ya nuna cewa idan ka sayar da wani abu Mallakin ka, aka baka kuɗi to Abun naka Yafi Kuɗin Daraja nesa ba kusa ba, Saboda Za’aiya Amfanuwa da abin da ka saida ɗin Amma shikuma kuɗin in anbarshi Ba zaiyi wannan Amfanin ba, Dan Haka Kuskurene muriƙa Fifita Takardar Kuɗi fiye da Dan Adam ko Albarkatun da Allah ya Azurtamu da su.

Sannan Daɗi akan Hakan, Hausawa Sunce Abin da ya Gagari Mai Kuɗi Shine, Abun da Bana Siyarwa ba, Kenan hakan Yanuna cewa Duk Arzikin ka idan akace Baza’asayar Maka Abu ba,To kai Talaka ne, kuma Talakan ma Yafi ka domin Shi ne mutumin da yafi Mallakar Abu, Saboda Zai saka Karfin sa Ya nema.

A ƙarshe Ina Amfani da wannan Dama wajan ƙira ga ‘yan uwana Matasa, Cewa da Mudaina Bari Ana amfani damu Saboda Haramtattun (KUƊAƊE) wajan Shiga aiyukan ta’addanci da kungiyoyin su Don kawai Za’abamu kuɗi,
*Shin Kuɗi Yafi Maka Ran Ɗan uwanka?
*Shin Wannan kuɗin da za’abaka zai Yanke maka Talauci ne ?
Shin Idan Anbaka wannan Kuɗin Zaka Samu damar amfanuwa dashi Cikin kwanciyar Hankali?
*Shin ko kasan cewa wanda yabaka wannan kuɗin ba masoyin ka bane maƙiyin kane?
*Shin Ko ka manta da cewa Duk kanin Kuɗin da kasamu dama Dukiyarka Saikayi Biyanin A inda kasamo Ranar Gobe ƙiyama?

Dafatan ‘Yan uwana Matasa Zaku Gane tare da Tashi ku nemi kuɗi na Halaliyar ku komin kankantar sa tahanyar Sana’o’i ko Leburanci,

Ya Allah Ka cire mana Masifar Son Kuɗi Ka Azurtamu da ƙalilan Masu Albarka Amin.

Daga Hussaini Abba Dambam Ƙaramar Hukumar Dambam Jihar Bauchi Najeriya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button