Tsaro

Shin Me Yasa Buhari Bazeyi Da Iris Deby Ba? Shi Yakoma Katsina YatareOsibanjo Yakoma Maiduguri.

Spread the love

Daga Kabiru Ado Muhd

Shugaban kasar chadi idriss deby ba Soja bane, don bai taba yin aikin Soja ba.

Amma a lokacin da ‘yan ta’addan suka addabi wasu yankuna na kasarsa da kashe kashen al’ummar da yake mulka fita yayi yabar hidan gwamnatin kasar ya jagoranci rundunar sojojin kasar zuwa yankunan da ‘yan ta’addan suke cin karensu ba babbaka yatare.

Idriss Deby bai baro dokar dajinnan ba sai da ya tabbatar ya karya lagon ‘yan ta’addan da suka addabi al’ummar da yake mulka.

Shugaba Buhari tsohon sojan yaki ne shi tun kafin yazama gwamna a Borno, kuma yayi shugaban kasa na mulkin Soja, ya ziyarci yakukkuna da dama.

Mai zai hana shugaba Buhari yayi kamar yadda shugaban kasar Chadi Idriss Deby yayi, shima ya tattara yanasa yanasa yadawo jihar Katsina mahaifarsa da zama, yayi bincike akan ta’addancin dake addabar ‘yan uwansa, tare da bincikar ainahin wadanda suke daukar nauyinsu da kansa a matsayin Sa na tsohon sojan yaki daya kware a harkar tsaro?

Sannan ya umarci mataimakinsa yemi osinbajo daya koma garin Borno, duk suci gaba da aiwatar da irin aikin da shugaban kasar Chadi Idriss Deby yayi a kasarsa.

Idriss deby fa ba Soja bane, bai tabayin aikin Soja ba, amma yayi haka.

Me yasa shugaba Buhari bazaiyi haka ba shida yake tsohon sojan yaki ne?

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button