Kungiyoyi

Shin Shugabancin Matasa Zai Iya Zama Mafita Ga Al’ummar Najeriya?

Spread the love

A gaskiya wannan tambaya tana da amsoshi biyu, wanda sune Eh da kuma A’a.

Duk da dai na kasance daya daga cikin jagororin kungiyoyi masu fafutukar gannin matasa sun karbi kasarnan a kowanne mataki.

Amma a gaskiya amsar A’a, dalili shine, bai zama dole a samu matasa suyiwa kasa aiki yanda akeso ba, domin kuwa zamu iya tabbatar da haka idan mukayi duba izuwa gwamnan jahar KogibYahaya Bello.

Gwmna Yahaya Bello dai ya kasance matashi ne, ga kuma wasu Sanatoci da Ƴan majalisar wakilai da kuma na Jihohi, amma sai ya kasance waƴannan bayin Allah babu wani abun da sukayi na azo a gani a inda suke wakilta, wasunsu ma irin ta’asar da suka tafka ba’a sami tsofafin da sukayi ire-iren su ba, kun ga ko a wannan fannin zan ce koda matashi ko tsoho, duk wanda akafi sa ran zaiyi aiki shi ya cancanta.

Idan kuma akazo inda nace Eh, shi matashi yana da tunani irin na zamani, akidojin sa irin na zamani, ba zai mulke ku yanda tsoho zai zo da irin akidar sa na tsofaffi ba, ba ma kamar yadda kimiyya da fasaha ta zama ruwan dare a duniya.

Amma, kai tsaye zan ce, gwamma a samu matashi mai adalci ya mulki guri akan asamu tsoho mai adalci, Allah Ya yi mana kyakyawan zabi. Amin.

Rtd. Comr. Amb Edet Zakariya Abubakar
Shugaban Kungiyan Matasa Dake Yaki Yaki Da Tashin Tashina Da Wanzar Da Zaman Lafiya.

Youth Crisis & Awareness Peace Forum (YCAF)

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button