Shine wanda yafi kowa arziƙi a tarihin Duniya, Alhaji Mansa Musa.
SHIN KO KA SAN WANDA YA FI KOWA ARZIƘI A TARIHIN DUNIYA?
Alhaji Musa Keita Mansa wanda ake kira Mansa Musa (wato Sarki Musa ) shi ne sarki na goma a jerin sarakunan daular ƙasar Mali wanda yanzu ta ƙunshi ƙasashen Mali da Murtaniya
An haifeshi a shekarar 1280C sannan ya mutu a shekarar 1337.
Binciken Masana kamar irinsu Jessica Smith da jaridar Time Magazine ya tabbatar da cewa a tarihin duniya babu attajiri sama da Alhaji Musa Keita. Adadin dukiyarsa ta wuce darajar kuɗi Dala biliyan 400.
•Alhaji Mansa Musa yana kyautar zinare tamkar yadda za ka buɗe randa ka bada kyautar ruwan sha
•Alhaji Mansa Musa da zai dawo wannan duniyar tare da dukiyarsa da duk waɗansu hamshaƙan attajiran da mu ke da su yanzu irinsu Bill Gates sai sun koma almajiran-almajiran gidansa
Babban abin sha’awa daya fi burge ni da Alhaji Mansa Musa guda huɗu ne :
1- Musulmi ne
2- Sannan ya yiwa musulunci hidima da dukiyarsa
3- Kasancewarsa ɗan nahiyar Afrika
4- Kuma baƙar fata.
Daga Mutawakkil Gambo Doko