Shugaba Buhari kadai ne Matsalar Najeriya~Matasan Arewa.
Gamayyar kungiyoyin Arewa ta Coalition Of Northern Groups, tace Babban Matsalar Kasar Nan Shine Shugaba Buhari.
Kakakin Ungiyar Abdul-azeez Suleiman ne ya sanar da Hakan.
Suleiman yace Matasan Arewa sun Yiwa Buhari ruwan Kuri’u a Shekarar 2015 da 2019 duk da bambancin Addini da Kabilu da muke dasu, Amma Arewa ta Zama koma baya ta Kowacce Fuska.
“Arewa ta zama tamkar filin daga, an kashe mutane Marasa laifi manoma fiye da mutum 100, a Zabarmari amma Gwamnati ko a kanta.
Yau Arewa mune Gidan Talauci, Yunwa, Rashin Tsaro, Boko Haram, Garkuwa da Mutane, ‘yan dadi Bindiga, Fyade da Sauran Fitin tinu dalilin Sakacin Gwamnati Inji Shi.
Ungiyar ta CNG, dai ta Tsaya tsayin daka wajen Nemawa Arewa da ‘yan Arewa ‘Yancin su duk da Barazanar da Suke fuskanta a Wajen ‘Yan Siyasa.
Ko a Watannin Baya Sai da Mahukunta suka kama Shugaban Ungiyar Nastura Ashir Sharif, a Birnin Katsina lokacin da Ungiyar ke Zanga zangar Lumana na Rashin Tsaro a Jihar.
Daga Ahmed T. Adam Bagas