Labarai

Shugaba Buhari Na Jagorantar Zaman Majalisar Zartaswa.

Spread the love

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari na jagorantar zaman majalisar Zartaswa a fadarshi dake Abuja yanzu haka.

Zaman wanda shine irinshi karo na 13 da ake yi ta kafar sadarwar Zamani ya samu halartar mataimakin shugaban kasar, Farfesa Yemi Osinbajo.

Akwai kuma sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha da Ibrahim Gambari wanda shine shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasar. Mun tattaro muku cewa an fara zaman ne da misalin karfe 10 na safiyar yau, Laraba.

Hakanan zaman na samun halartar Ministoci 6 inda sauran suke halartar zaman ta kafar Sadarwar Zamani.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button