Labarai

Shugaba Buhari ya amince da amfani da Tiriliyan 2.3 dan hana Najeriya fadawa matsin tattalin arziki

Spread the love

Shugaban kasa,Muhammadu Buhari ya amince da Naira 2.3 trillion dan a sakasu a cikin harkokin tattalin arzikin Najeriya dan haka tattalin arzikin rugujewa saboda barazanar cutar Coronavirus/COVID-19.

Ministar Kudi, Zainab Shamsuna Ahmad ce ta bayyana haka a ganawar da ta yi da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan zaman majalisar zartaswa a jiya.

Ta bayyana cewa wannan shawarace da kwamitin tattin arziki, karkashin mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya bayar a matsayin hanyar ceto tattalin arzikin Najeriya daga Rushewa.

Tace tsarin zai taimaka wajan amfani da kayan da aka kera a Najeriya da kuma tallafawa ‘yan kasuwa kanana da matsakaita.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button