Labarai
Shugaba Buhari ya aminta da Sakin Naira Biliyan goma 10bn ga hukumar Qidaya ta kasa
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da sakin naira biliyan 10 ga hukumar kidaya ta kasa, NPC, domin ci gaba da shata iyaka a yankin, EAD, a sauran ragowar kananan hukumomi 546 na kasar. Mukaddashin Shugaban NPC din, Dr. Eyitayo Oyetunji ne ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Abuja. A cewarsa, shugaban kasar ya kuma amince da karin naira biliyan N4.5 don sanya shi a cikin Kasafin Kudin na 2021 don kammala aikin.