Labarai
Shugaba Buhari ya aminta da Sakon Bilyan 8.9bn ga ma’aikatan lafiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da karin N8.9bn a matsayin alawus na hadari ga dukkan ma’aikatan kiwon lafiya. Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF) kuma Shugaban Rundunar Shugaban Kasa ta PTF a kan COVID-19, Boss Mustapha, ne ya sanar da hakan yayin taron tattaunawa da ’yan jarida game da rundunar a Abuja.
Ya kumayi magana kan kungiyar likitocin kasa (NARD) na barazanar da wasu kwararru a bangaren kiwon lafiya sukayi na yajin aiki kwanakin da suka gabata. “Ina mai farin cikin sanar da ku cewa, Shugaban Kasa cikin karimci ya amince da karin N8.9bn na alawus din COVID-19 ga dukkan ma’aikatan kiwon lafiya. Bugu da kari, za a bai wa sayen kayayyakin kariya na sirri (PPE) na asibitoci da cibiyoyin kebewa fifiko, ”in ji Mustapha.