Shugaba Buhari ya Baiwa Dan Takarar Gwamnan Ondo a APC Tutar Takara.
A yau Juma’a ne, Shugaba Muhammadu Buhari ya bukaci jam’iyya mai mulki ta APC, da ta yi aiki tukuru tare da tabbatar da adalci a yayin gudanar da zabe, yayin da dan takarar gwamna na jam’iyyar, Rotimi Akeredolu, SAN, yake son Komawa kujerarsa a karo na Biyu.
Shugaban kasar, wanda ya gabatar da tutar jam’iyyar ga dan takarar a Fadar Shugaban Kasa, ya ce matakan sulhun da akabi a jam’iyyar reshen jihar zai samar da nasarar ga dan takarar fiye da yadda ya samu a zangonsa na farko.
Yayin da yake tabbatar wa Akeredolu, cikakken goyon bayansa Shugaba Buhari, ya ce a yi zaben lumana da adalci da ke nuna muradin mutane ya kamata ya zama mafi rinjaye, yana mai kira da a bi ka’idojin Hukumar Zabe ta Kasa mai zaman kanta da kuma ladabi ga Cibiyar Kula da Cututtuka ta Najeriya.
Shugaba Buhari ya lura cewa tsarin jam’iyyar na sasanta bambance-bambance ya fi tasiri, kuma za a dore dashi ne don karfafa alakar, da tsara manufofin jam’iyyar a matsayin abin da zai kawo cigaban jama’a.
Dan takarar na APC ya gabatar wa Shugaban ne ta hannun Shugaban Kwamitin riko na Jam’iyyar, Mai Mala Buni, wanda kuma shi ne Gwamnan Jihar Yobe.
Ahmed T. Adam Bagas