Shugaba Buhari ya bayarda umarni ga NYSC ta saka ‘yan bautar Kasa Acikin Inshorar lafiya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya umarci hukumar bautar kasa ta kasa, NYSC, da ta tabbatar da sanya ‘yan yi wa kasa hidimar a cikin shirin inshorar lafiya ta kasa.
Darakta-Janar na NYSC, Shuaibu Ibrahim ne ya bayyana hakan a ranar Litinin a Abuja. A cewarsa, NYSC ta zage damtse tare da hukumomin tsaro don tabbatar da tsaron mambobin bautar kasa a duk inda suke yi a kasar. Ya ce tare da tattara masu yi wa kasa hidiman 300,000 da ake yi duk shekara, babu shakka NYSC, “har yanzu ita ce babbar hanyar da za a bi wajen koyar da matasan Nijeriya a matsayin direbobin hadin kan kasa da ci gabanta.”
Ya kara da cewa; “Ina son yin amfani da wannan damar domin sake bayyana godiyarmu ga jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki kan goyon bayan da suka ba mu.
“Bugu da ƙari, shirin ya kammala shiri tare da NHIS don yin rajistar mambobin bautar a cikin NHIS bisa ga umarnin shugaban kasa Mun kuma kashe kudade masu yawa kan mahimmancin kiwon lafiya na mambobin bautar, gami da biyan kuɗin likita.” Rahotan daily Nigerian