Labarai

Shugaba Buhari Ya Bayyana Inda Zai Mayar Da Hankali A Sauran Shekaru 3 Da Suka Rage Masa.

Spread the love

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana bangarorin da zai fi baiwa fifiko a saurannshekaru 3 da suka rage masa ya kammala wa’adinsa na 2 akan Kujerar Mulki.

Shugaban ya bayyana cewa zai maida hankali wajen rage talauci da kuma habaka harkar kiwon lafiya. Hakan na kunshene cikin sanarwar da me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesina ya fitar.

Shugaba Buhari ya karbi takardun fara aiki na jakadun kasashe 8 da aka turo zuwa Najeriya inda a nan ne yayi wadannan bayanai.

Shugaban ya bayyana bangarori 9 da yace nan ne gwamnatinsa zata maida hankali nan da shekaru 3 da suka rage, ya kuma bada tabbacin cewa, kasar zata zama guri me kyawun yanayin zuba jari ga ‘yan kasuwa.

Shugaban yace zai dira kasar akan tsari me dorewa da kuma kula da jama’a ulyanda ya kamata, fadada harkar noma dan samar da abinci, samar da Makamashi, inganta ayyukan Sufuri da sauyan ayyukan ci gaba, fadada harkar kasuwanci da karfafa dogaro da kai da fadada masana’antu,samar da ingantaccen ilimi, karfafa tsaro, Samar da yanayi me kyau na yaki da cin hanci.

Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button