Tsaro
Shugaba Buhari Ya Bayyana Manyan Dalilai 2 Da Suka Hana Kawo Karshen Yan Ta’adda.
Daga Comr Yaseer Alhassan Gombe
Shugaban kasa,Muhammadu Buhari a ganawar da yayi da gwamnonin Arewa Maso gabashin Najeriya ya bayyana dalilai 2 da suka hana kawo karshen ‘yan ta’adda a Najeriya.
Shugaban bayan taron da yayi da gwamnonin da shuwagabannin tsaro ya bayyana cewa rashin isassun kudi/kayan aiki a gwamnatinsa da zuwan cutar Coronavirus/COVID-19 sun gurgunta aikin samar da tsaro a kasarnan.
Me magana da yawun shugaban kasar, Femi Adesinane ya bayyanawa manema labarai da hakan inda yace amma duk da haka gwamnatinsa ta yi kokari wajan tsaro.
Yace lura da matsalolin da suka gada sun yi kokari sosai kuma jama’ar yankin Arewa maso gabas din zasu shaida haka.