Tsaro
Shugaba Buhari Ya Gargadi Masu Zanga-zanga A Katsina.
Daga Kabiru Ado Muhd
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi kira ga jama’ar jihar Katsina da su kara hakuri, Jami’an tsaron Najeriya sun daura damarar magance yawaitar kashe kashen.
Sannan ya gargadi masu zanga-zangar cewa yin zanga-zangar ba mafita bace, domin zata kawo tsaiko a yunkurin da Jami’an tsaron Najeriya sukeyi Na murkushe ‘yan ta’addan.
Shugaban yayi wannan bayanin ne bayan ya gama kallon zanga zangar da aka gudanar yau a jihar Katsina ta kafar talabijin a fadarsa dake babban birnin tarayya Abuja.