Shugaba Buhari ya gargadi ‘yan Ta’addan katsina da Babbar murya a wata ganawa da Shugaban yayi da gwamnan jihar katsina Rt Hon aminu bello masari fadarsa asi rock dake abuje yasha alwashin kawo sabbin tsare tsare ga jami’an tsaron dake yaki da ya ta’addan domin ganin an kawo karshen Ta’addanci a jihar ta katsina haka zalika shugaba buharin yace yanzu haka zabi biyu ne ya ragema ‘yan Ta’addan ko dai suyi suranda su ajiye makamansu ko kuma su fuskanci fushin Gwamnati.
Dayake magana ta bakin mai magana da yawunsa malam garba shehu yace jami’an tsaron da suke aikin yaki da ‘yan Ta’adda a jihohin katsina zamfara sokoto niger da kaduna zasu kasance na wucin gadi ne lokaci lokaci za’a rinka canja masu waje…