Shugaba Buhari Ya Kafa Kwamitin Da Zai Bunkasa Najeriya Nan Da Shekaru 30.
Shugaban Kasar Muhammadu Buhari, ya kafa kwamitin bunƙkasa ƙkasar nan da shekaru 30 masu zuwa, mai suna Agenda 2050, ƙarƙkashin jagorancin dan kasuwar nan Atedo Peterside da kuma ministar kudi da kasafi da tsare-tsare, Hajiya. Zainab Ahmed.
Ana sa ran wannan muradin na Buhari na shekarar 2050 zai cire ‘yan ƙasar mutum miliyan 100 daga talauci sakamakon hasashen da Bankin Duniya ya yi na cewa nan da 2040 adadin ‘yan Najeriya zai kai miliyan 400.
Kwamitin zai gaji shirin Najeriya na Vision 2020 wanda gwamnatin marigayi Umar Musa Yar’adua ta ƙaddamar a shekarar 2009, da kuma shirin ERGP na 2017 da aka kafa domin farfaɗo da tattalin arziƙin Najeriya.
Kwamitin da gwamnatin ta kafa zai ƙunshi gwamnoni shida, daya daga cikin kowane yanki na ƙasar, da kuma ‘yan majalisa da sanatoci da ministoci da wakilan hukumomi da na manyan jam’iyyu, da ‘yan kasuwa da ‘yan jarida da dai sauransu.
Idan bamu manta ba Watannin Baya ma Gwamnatin Tarayya tayi Ikirarin Ta fitar da ‘Yan Najeriya miliyan 100 daga Talauci.
Daga Ahmed T. Adam Bagas