Labarai

Shugaba Buhari ya karrama Sani Kila da lambar Yabo ta Kasa Mafi girma.

Spread the love

Tsohon Shugaban Hukumar Kula da shige da fice na Kasa reshen Jihar Kano da kaduna Mr Sani Liman Kila ya sami lambar karramawar kasa, Member of the Order of the Federal Republic (MFR) daga Shugaban Kasar tarayyar Nageriya Muhammadu Buhari.

Mr Kila Ya sami wannan Lambar Yabo ne daga Ma’aikatar ayyuka na musamman da harkokin gwamnatocin tarayya (Federal ministry of Special Duties and Inter-governmental Affairs.

karramawar kasa ta MFR a Nageriya ta kasance daga cikin manyan lambobin Yabo Mafi Girma da ake baiwa ‘yan Najeriya da ma’abota hidima ga Najeriya a kowacce shekara. Dokar karramawa ta kasa mai lambar doka 5 wacce aka Samar a shekarar Alif 1964, a lokacin Jamhuriyyar Najeriya ta Farko, duk domin karrama ‘yan Najeriya da suka yi hidima don amfanin al’umma musamman wa’yanda aka tabbatar sunyi hidima bisa gaskiya da Amana tare da kwazo a lokacin gudanar Ayyukan su.

Waɗannan lambobin yabo sun bambanta da karramawa wani ɓangare ne na tsohon tsarin mulkin ƙasar, wanda keɓaɓɓe ne amma kuma bisa ƙa’ida Karramawar kasa ita ce mafi kololuwar karramawa ko karramawa da dan kasa zai iya samu daga kasarsa amatsayin Sakamakon Hidima ga kasa.

A shekara ta 2004 Wani mawallafi Dan Najeriya Chinua Achebe ya samu wannan lambar yabo ta kasa daga gwamnatin Najeriya amma ya ki amincewa ya karba saboda yana jin takaicin yadda gwamnati ke tafiyar da mulkin Najeriya a lokacin.

Sani Liman Kila wanda ya kasance sama da shekaru talatin amatsayin Jami’in Hukumar Kula da shige da fice na Kasa (Immigration Service) wanda harya Kai ga samun matsayin Kwanturola (Comptroller) a Hukumar kafin ya ajiye aiki ya kasance Shugaban Hukumar reshen Jihar Kaduna da Kano amatsayin Kwanturola.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button