Shugaba Buhari Ya mallakawa ‘Yan Majalisa Bilyan 128bn.
Gwamnatin Shugaba Buhari zata dauki nauyin Majalisar Tarayya da kudi Naira biliyan 128 a shekarar 2021 kamar yadda Shugaban kasa, Manjo Janar Muhammadu Buhari (mai ritaya), ya yarda cewa Gwamnatin Tarayya na kashe makudan kudade ba bisa ka’ida ba yayin gabatar da Kasafin Kudin 2021 a ayau hadadden taron Majalisar Kasa a ranar Alhamis, Shugaban Yace ya lura cewa har yanzu kudin ma’aikata shi ne mafi girman bangaren kashe kasafin kudi. Shugaban ya dora alhakin hakan a kan ma’aikatan bogi) da alawus-alawus mara izini a Ma’aikatu da Hukumomi suke gabatar wa. Don haka, ya umarci shugabannin MDAs domin daukar mataki..
A Masa bangaren Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, ya ce Majalisar Tarayya a shirye take ta zartar da Dokar Kasafin Kudin na 2021 kafin karshen shekarar 2020.
Kasafin Kudi: Majalisar Kasa ta rabauta da N128bn na 2021