Wasanni

Shugaba Buhari Ya Yi Farin Ciki Da Komawar Osimhen Napoli.

Spread the love

Mataimakin jakadan Najeriya a Italiya, Franklin Ogunyemi, ya bayyana cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi farin ciki da shawarar dan wasan Super Eagles, Victor Osimhen na shiga kungiyar Kattai ta Serie A, ta Napoli.

Ya kuma ce daukacin ma’aikatan diflomasiya a kasar suna murna da matakin da dan kungiyar mai shekaru 21 ya dauka.

Ogunyemi ya fadi haka ne lokacin da ya bayyana a Rediyon Kiss Kiss, gidan rediyon Naples mai asali.

A cewarsa, “Ofishin jakadancin Najeriya gaba daya wanda Ambasada Yusuf Jonga Hinna ke jagoranta, yana matukar farin ciki da komawar Victor Osimhen zuwa Naples. “Mun san cewa shugaban kasar mu Muhammadu Buhari, ya yi farin ciki da wannan sauyi.

Osimhen matashi ne amma kuma dan wasan gaba sosai. ” Osimhen ya zira kwallaye 18 a kakar wasa ta farko tare da Lille, inda ya jawo hankalin kungiyoyi daga manyan kungiyoyin Ingila da LaLiga na Spain da sauran manyan kungiyoyin wasannin.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button