Shugaba Buhari Zai Yi Tafiya Kasar Guinea Bissau Yau Alhamis.
Shugaba Muhammadu Buhari zai yi tafiya kasar Guinea Bissau, daga birnin tarayya Abuja ranar Alhamis, 24 ga Satumba halartan taron murnar shekaru 47 da samun yancin kasar.
Mai magana da yawunsa, Femi Adesina, ne ya sanar da hakan a shafin fadar shugaban kasa na manhajar Facebook.
Ya bayyana cewa shugaban kasan zai hadu da takwarorinsa na kasan Cote d’ Ivoire, Rwanda, Mauritania, Togo da Liberia.
Yace: “A birnin Bissau, shugaba Buhari zai kaddamar da sabuwar titin da aka sanyawa sunansa domin karramashi. “Bayan haka shugaban kasar da sauran shugabannin kasashen da aka gayyata zasu halarci liyafar da shugaban Guinea Bissau, Umaru Sissoco Embalo, da ya shirya.
Shugaban kasan zai samu rakiyar manyan jami’an gwamnati wanda ya hada da ministan harkokin waje, Geofrey Onyeama; ministan tsaro, Manjo Janar Bashir Salihi Magashi (Mai ritaya); mai bada shawara kan tsaron kasa, Babagana Monguno; da dirakta Janar na hukumar NIA, Ahmed Rufai Abubakar.
A karshe, Adesina ya bayyana cewa shugaban kasa zai dawo Najeriya ana kammala taron.
Daga Amir sufi