Labarai

Shugaba Tinubu ya kaddamar tallafin naira dubu sab’in da biyar biyar N75,000 ga mutane milyan Sha biyar a Nageriya

Spread the love

Shugaban Kasa Tinubu Ya Kaddamar da Sabbin Shirin nan na Tallafin Kudi na Hope ga Magidanta Miliyan 15 don tunawa da Ranar Kawar da Talauci ta Duniya ta 2023.

Shugaban Kasa Bola Ahmad Tinubu Ya dauki matakin ne ta hanyar kaddamar da rabon Naira 25,000 ga gidaje miliyan 15 na tsawon watanni 3.

Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ne ya kaddamar da taron a madadin shugaban kasa a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Da yake jawabi a lokacin kaddamar da shirin, shugaban ya zayyana matakai daban-daban da gwamnatinsa ta dauka na inganta rayuwar Al’umma tare da kawar da talauci a kasar.

Wadannan, a cewar shugaban, sun hada da samar da tsare-tsare da taswirori na wani yunkuri na kawar da talauci a Najeriya, da samar da ajandar Renewed Hope na bayar da agajin jin kai da kuma kawar da fatara.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button