Labarai

Shugaba Tinubu ya nada kakakin majalissar wakilai Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar sa.

Spread the love

Bola Tinubu ya nada kakakin majalisar wakilai mai ci Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar sa.

Olanrenwaju Smart Wasiu, shugaban ma’aikatan Gbajabiamila ne ya tabbatar da hakan.

Smart ya bayyana cewa shugaban ya nada Gbajabiamila ne bayan shafe sa’o’i da dama na ganawa da tuntubar juna.

An ce shugaban ya yanke shawarar zabar Gbajabiamila ne bayan da ya tantance dukkan masu neman mukamin a tsakanin magoya bayansa.

Hon. Femi Gbajabiamila wanda har yanzu bai karbi takardar shaidar cin zabe daga hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) ba, dole ne ya hakura da zabensa a majalisar wakilai a karo na shida.

Haka kuma wannan ci gaban zai sake haifar da wata dama ga sauran masu son tsayawa takara a jam’iyyar da suka kawar da burinsu na wakiltar mazabar Surulere 1 a majalisar wakilai.

A cewar Smart, Gbajabiamila ne shugaban ya zabo shi ne bayan ganawar karshe da masu ruwa da tsaki da aka kammala a safiyar Alhamis a fadar Villa da ke Abuja.

Ya kara da cewa Tinubu ya yanke shawarar zabar shugaban majalisar ne domin ya samu wanda zai taimaka masa ya jawo ‘yan majalisa a majalisar dokokin kasar su amince da shawarwari da manufofinsa.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button