Shugaba Tinubu ya roki Jami’ar Chicago Dake Amurka da Karsu saki wasu bayanai akansa Kawai a bawa Atiku iya shedar karatu.
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, ya Amince da bai wa wani alkali a kasar Amurka takardar shaidar kammala karatunsa na jami’a, Ga Abokin hamayyarsa Atiku Abubakar. Amma Tinubu ya roki mai shari’a Nancy Maldonado da ta toshe duk wasu Bayanai Dangane Dashi.
Bukatar Tinubu tazo ne a Yau Litinin a wani ɓangare na takaddamar shari’a da ake yi a Kotun Amurka dake Arewacin Gundumar Illinois dake Chicago.
Atiku Abubakar ne Ya Shigar da ƙarar, Wanda ke neman Tabbatar da cewa Tinubu bai cancanci zama Shugaban kasa ba duk da cewa ya ci zaɓe a watan Fabrairun 2023.
Matakin na Tinubu na sakin satifiket ɗin nasa na Zuwa ne bayan da ɗan kaɗan ya kaucewa bayyana cikakken bayani a Ranar 21 ga watan Satumba Inda ya roke shi cewa hakan zai jawo masa mummunar illa.
Sakamakon shari’ar na iya yin tasiri sosai ga Harƙoƙin Siyasar Tinubu. Idan har Atiku Abubakar zai iya tabbatar da cewa Tinubu bai cancanci zama shugaban kasa ba, za a iya tsige Tinubu Daga Mukaminsa kuma a naɗa Atiku Abubakar a Matsayin Shugaban ƙasa.
Har ila yau, al’amarin na sa idon ‘yan Najeriya, waɗanda ke ƙoƙarin Ganin ko za a tuhumi Tinubu kan wasu kura-kurai da ake zarginsa da aikatawa a tarihin karatunsa.