Labarai
Shugaba Tinubu ya ware buhunan shinkafa 1,200 ga kowane minista domin rabawa a wani bangare na ayyukan agaji.
Ministan ma’adanai Dr. Dele Alake ya bayyana cewa buhunan shinkafa 1,200 da fadar shugaban kasa ta bayar a matsayin tallafi ga al’umma za a raba shi ne kawai ga tsofaffi a jihar.
Alake ya bayyana haka ne ta wata sanarwa da mai taimaka masa na musamman kan harkokin yada labarai, Segun Tomori ya fitar, wanda aka bayyana a Ado Ekiti ranar Lahadi.