Labarai

Shugaba Tinubu Ya Zama Shugaban ECOWAS

Spread the love

Tinubu ya gaji Umaro Embalo na Guinea Bissau a matsayin shugaban ECOWAS.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya zama sabon shugaban kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka ECOWAS.

“Za mu dauki dimokuradiyya da muhimmanci, Dimokuradiyya tana da matukar wahala amma ita ce mafi kyawun tsarin gwamnati,” in ji shi yayin da ya fito ranar Lahadi a Guinea-Bissau.

Tinubu ya gaji Umaro Embalo na Guinea Bissau a matsayin shugaban ECOWAS.

An sanar da zaben na Tinubu ne a zaman taro na 63 na shugabannin gwamnatocin kasashen ECOWAS.

Taron gamayyar kasa da kasa karo na 63 shi ne ganawa ta farko da shugaban kasar ya yi a nahiyar Afirka tun bayan hawansa mulki a ranar 29 ga Mayu, 2023.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button