Kasashen Ketare

Shugaban Ghana, Akufo Addo, Ya Zama Sabon Shugaban ECOWAS.

Spread the love

Nana Akufo-Addo, Shugaban Jamhuriyar Ghana, an zabe shi a matsayin sabon Shugaban Kungiyar a taron ECOWAS na 57 da ke gudana yanzu haka a Yamai, Jamhuriyar Nijar.

A yayin taron, Shugaban Najeriya Buhari, ya yi kira ga shugabannin Afirka da su daina tsawaita lokacin da suke yi a kan wannan kujerar, yana mai cewa hakan na zama silar haifar da matsala a cikin Kungiyar.

Addo ya karbi ragamar kungiyar a dai dai lokacin da kungiyar ke kai ruwa rana, da Sojojin Kasar Mali da sukayi Juyin Mulki a Kasar, Inda suka Nemi sojojin da su maida mulkin ga Tsohon Shugaban Kasar, Sojojin Sukaki amincewa da hakan.

Daga bisani ECOWAS Ta bukaci sojojin da suyi shekara 1 tal, akan mulki su mika Mulkin ga Farar Hulla a kasar, Sai dai Sojojin Sunce Shekaru 3 zasuyi kana su mika mulkin ga farar Hula.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button