Shugaban INEC, Mahmood Yakubu zai sauka Ranar Litinin.
Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu, zai mika ragamar hukumar ga wani kwamishina na rikon kwarya har sai Majalisar Dattawa ta amince da sake nada shi a matsayin shugaban INEC ko kuma akasin haka.
Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya sake nada Yakubu, ya mika sunansa ga Majalisar Dokoki ta Kasa don tabbatar da shi, inda wa’adinsa na farko zai kare a ranar Litinin, 9 ga Nuwamba.
Ana sa ran zai mika ragamar hukumar ga kwamishinoni wadanda wa’adinsu bai kare ba.
Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), babbar jam’iyyar adawa a Najeriya, ta yi imanin cewa sake nada Yakubu a matsayin shugaban INEC zai zama wani hanzari ga sahihin zabe a Najeriya.
Shugaba Buhari ya fara nada Farfesa Yakubu a watan Nuwamba na shekarar 2015.