Shugaban Karamar Hukuma Ya Yi Aikin Da Gwamnoni Da Yawa Suka Kasa..

Daga Auwal Ahmad Wali..
Hanyar Mayo-Nguli Zuwa Belel Zuwa Maiha Hanya Ce Mai Nisan Kilo Mita 108KMs.
Hanyar Ta Yi Shekaru Masu Yawa Ba A Binta Saboda Lalacewar Da Tayi. Al’ummar Yankin Sun Yita Mika Koke Ga Mahukunta Amma Anki A Duba Koken.
Kwatsam A Wannan Karon Kuma Sai Allah Yakawo Musu Gwamnatin Masu Adalci, Gwamnatin Masu Kula Da Damuwar Talakawa, Wato Gwamnatin PDP Karkashin Jagorancin Mai Girma Gwamna Umaru Fintiri, Inada Mai Girma Shugaban Karamar Hukumar Maiha Dr. Idi Aminu, Rumbun Adamawa, Kuma Turakin Pakka Yafara Aikin Wannan Katafariyar Hanyar….
Aikin Hanyar Yana Tafiya Cikin Sauri, Kuma Ana Aiki Dare Da Rana Domin A Sami Damar Kammala Aikin Da Wuri. Tun Daga Yadda Aka Faro Aiki Za Ka Gane Cewa Ana Aiki Mai Inganci, Kai Abin Dai Sai Wanda Yagani.
Godiya Mai Tarin Yawa Ga Mai Girma Chairman Dr. Idi Aminu Rumbun Adamawa, Turakin Pakka…
Daga Auwal Ahmad Wali.


