Rahotanni

Shugaban Kasa Buhari Ka Kama Ministan Shara’a~ Inji Wani Lauya

Spread the love

Wani lauya Kabir Akingbolu yayi kira ga shugaban kasa, Muhammadu Buhari da ya kama Ministan Shari’a, Abubakar Malami SAN saboda sawa da yayi a Saida wasu jiragen ruwa makare da mai da yayi ba bisa doka ba.

Malami ya baiwa kamafanin Omo-Jah Nigeria Ltd. umarnin sayar da man da aka kwace sai dai kamfanin ana zarginsa da satar Mai Ganga dubu 12 wanda maganar na kotu. Malami yace tunda dai ba’a kama wannan kamfani da laifi ba, zargine ake masa, babu wani aibu idan an bashi aikin sayar da man.

Lauyan yace tunda dai Malami ya amince da cewa shi ya bada umarnin sayar da man ba tare da Amincewar hukumar EFCC ba, to ya kamata a kamashi a bincikeshi.

Malami da yana shan Suka a yan kwanakin nan kamar yadda Jaridar Sahara Reporters ta buga Poton wani makeken gida da akace Malami ne ya sayawa Dansa har naira Miliyan 300 a Birnin Tarayya, Sannan Yana Hawa Mota da ta haura Miliyan 30.

Ko a Daren Jiya Sahara Reforters din Ta Sanya Bidiyo Wani Makeken Gini da Ba’a kammalaba A Shafinsu Na Facebook Cewar Hotel ne Mallakin Ministan Shara’a Abubakar Malami ne a Jabi dake Abuja, Sunce Wannan Hotel din ya Lakume Biliyoyin Nairori, Sai dai Jaridar tace Wani Na Kusa da Ministan ne ya Sanar dasu Hakan.

Ahmed T. Adam Bagas

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button