Shugaban kasa na bukatar goyon bayan kowa da kowa don shawo kan mugwayen sojojin da ke cikin kasarnan, in ji Gwamna Tambuwal.
Gwamna Tambuwal ya bayyana wadanda ke adawa da gwamnatin Buhari.
Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Tambuwal, ya ce wadanda ya bayyana a matsayin mugayen sojoji suna fada ne da al’ummar kasar nan a karkashin Shugaba Muhammadu Buhari.
Tambuwal ya ce Shugaban kasar na bukatar goyon bayan kowa da kowa don shawo kan mugayen sojojin da ke cikin kasar.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin lokacin da ya karbi bakuncin Shehun Bama wanda ya kai masa ziyarar ban girma.
A cewar sa, “Dole ne mu hada kai a matsayin mu na mutane kuma a matsayin mu na shugabanni, sannan mu marawa gwamnatin tarayya baya domin samar da zaman lafiya a yankunan da ke fama da rikici a fadin kasar nan.
“Za mu ci gaba da mara wa Shugaban kasa baya don shawo kan mugayen dakarun da ke kokarin tayar da zaune tsaye a kasarmu.”
Tambuwal ya nuna farin cikin sa cewa Bama, wacce a da ita ce cibiyar kungiyar ta’addanci ta Boko Haram, tana samun kwanciyar hankali a hankali.
Gwamnan, ya ce har yanzu masarautar tana da sauran rawar da za ta taka, yana mai cewa, “Dole ne ku goyi bayan dan uwanku, Gwamna Babagana Zulum da gwamnatin tarayya kan duk abin da suke yi na daidaita jihar da kasar nan.